Alajabi kasha na II (2)--- Alajabi kasha na II(2)
Shi kuma wannan wani abin Ajajabi ne ya faru Tsakanin wani Dattijo da wani Matashi dan Mai Arziki,a dai-dai wani round about da misalin karfe 10:00 na safe, yaron yana cikin tukin motar Baban sa cikin sauri zai shiga Round,a dai-dai wannan lokaci Dattijon nan ya riga ya shiga kafin yaron wanda shi yaron yakamata ya tsaya saboda an riga shi shiga,cikin sauri sai ya bugawa mai motar nan,anan fa Go-slow ya hadu Motoci ba gaba ba baya,sai Horn kake ji ta ko,ina,Yaron nan yana fitowa bai ce da dattijon nan komai bai sai ihu da kyara agaban Yellow fifa,dattijon nan bai ce komai sai yace da masu yellon kaya su auna su tafi dasu Station domin abi masa hakkin sa saboda yaron yana cewa Babansa me iya saya masa sabuwar mota ne suje station din,suka je aka dauki bayanai dattijon nan yace shi zai tafi,idan mahaifin yaron yazo akirawo shi ko kuma in angyara masa mota sai ya dawo ya dauka.
Mahaifin yaro yazo yana ta fada ya na cewa damme za,a kulle masa yaro akirawo mai motar yazo ya fadi kudin motar ya biya,Zuwan sa keda wuya sai yaji wannan kalamai na fitowa daga bakin Uban yaro.sai ya shiga ya zauna,zaman sa keda wuya sai Uban yaron nan ya mike yana kallon Dattijon nan,kallon kamar yasan shi, Ya tambaye shi Bawan Allah kamar nasan ka yace ba mamaki,kai mun kama da Allah Abdullahi wanda na zauna kusa dashi a unguwar Sarari kusa da Yan gadi,yace nine sai Uban yaron nan ya sunkuyar da kai,ya yi dogon numfashi, ya kalli yaron,ya kalli ma,aikata ya kara kallon sa Y ace, kaine lokacin da na haifi da,na na fari bani da yadda zanyi ko kudin asibiti na kasa biya ka biya mun, kayi ragon suna ,ka sayawa yaron kayan jarirai,da duk abin da akaci aka asha ranar suna,Yace Nine ai ni dana shigo naga ne ka.ya kalli Allahajin yace to wannan Yaron da ya buga maka mota ai shi ne Yaron,,,….----- Sai kowa ya yi Tsit ba bu me cwa UFFAN.
In kai ne Dattijon ya ya zaka yi,kuma in kai ne uban yaron zaka chanja wa Dattijon Motar ko baza ka chanja.?kuma wane mataki yakamata ya dauka akn Dan na Sa?

Views: 166

Reply to This

Videos

  • Add Videos
  • View All

Music

Loading…

Events

© 2017   Created by Dandalin Tallafawa Matasa.   Powered by

Badges  |  Report an Issue  |  Terms of Service

Live Support