Facebook

Dandalin Tallafawa Matasa | Promote Your Page Too

Comment

You need to be a member of Dandalin Tallafawa Matasa to add comments!

Join Dandalin Tallafawa Matasa

Comment by Abdulrahman Salis Rahama on June 6, 2016 at 11:40pm
Slm .....
Ina taya dukkan alummar musulmai murna
da zuwan watan ramadan ALLAH y hadamu da dukkan alkairin dake cikinsa AMEEN.
Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on January 7, 2014 at 3:41pm

Al,ajabi--------Al,ajabi-----Al,ajabi
Yau ne da safe ina cikin mota na dawo daga daurin aure sai naga wani abin mamaki ,nazo zan gifta wani mai mota kirar Honda Accord ta zamani sai naga wani mai keken napep yana zagin wannan mai mota har takai sun yi fakin din Motar da kuma Babur din,mai keken napep ya ya fito ya tin kari mai mota yana tsaye har ya kama kwalar rigarsa ta wajen taga sai yaji an kirawo sunan sa ashe wanda ke gaban motar nan kanen baban sa ne,kuma a bayan motar Mahaifiyar sa ce akwance tana ta nishi hannuwan ta a daure da bandaji da kafafuwanta wani na rike da ita,sai yayi shiru ya rasa mai zaice,daga karshe dai ya yi ta maza ya ce mai ya faru mahaifiyar sa ta shi ga wannan hali,sai ta ka da baki tace da shi kai mukayi da kai zaka zo ka kaini gidan kanwar ka, sabo yau ne ake sunan dan ta na fari,kuma kasan nike zuwa na dora mata ruwa, nayi jira baka zoba sai na fito zan tare mai babur irin naka,wajan tsallaka titi sai wani mai babur din irin naka ya buge ni har na fadi,kuma ya bi ni ya rufe ni da duka,sai da mutane suka yi tara--tara a ka kamashi an kai shi wajen Hukuma yana can tsare,shi kuma wannan mai motar ban sanshi ba ya zo shi gewa ne yaga abin da ya faru shi ne ya dauke ni ya kaini asibiti aka dora ni kuma ya biya mun magani yanzu muna hanyar mu ta komawa gida ne kai kuma kazo ka goge masa mota ya yi magana kuma kake ta zagin sa har kazo kaci kwalar rigarsa sai uwarnan ta fasheda kuka ta kara fashewa da kuka.........

In kai ne ya ya zakayi,kuma me zaka ce da mutumin nan? Sannan kuma in kai ne Mai motar wane mataki zaka dauka. Sannan wane darasi mai wannan Babur ya gani da idon sa.?

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on December 3, 2013 at 10:32pm

Salam,alaikum yan uwa ga ci gaban mu labarin mutane ukun da muka fara bada labarin su a baya, .
kashi na biyu,,,,.
SHI KUMA WANNAN WANI MUTUM NE WANDA BAIDA SANA,A SAI AIKIN LABURAN CI NA GINI,AMMA IN YAGA RANA TA FITO BAI SAMU AIKIN GININ BA YANA IYA KO WACCE SANA,A HAR DAKO MA YANA IYA YI IN YA SAMU WATA RANA YA SHIGA TSAKA MAI WUYA,MATAR SA NADA CIKI,YA,YAN SA KUMA AN KORO SU DAGA MAKARANTA DOMIN BAI BIYA KUDIN TERM DIN DA YA WUCE BA BALLE NA TERM DIN DA AKE CIKI.
SAI YA YI SAMMAKO YA TAFI INDA SUKE TARUWA DOMIN KO YA SAMU ASAKA SHI A CIKIN AIKIN DA ZA,AYI A WANNAN YINI ,SAI YAI RASHIN SA,A ,WASU SUN RIGA SHI ZUWA SUN JE BAYAN AN IDAR SALLAR ASUBA.HAR SUN HAU MOTA ZASU TAFI KAUYEN DA ZASU JE ZUBA KANKARE.
RAN SA YA BACI SOSAI YAYI KOKARIN WANI WAJEN SHIMA BAI SAMU BA,YAJE KASUWA DOMIN NEMAN DAKO HAR YA SAMU DAKON WASU SUKA CE BASU SAN SHI BA SABODA HAKA KAR KAYAN MUTANE SU BATA, BAZA,A BASHIBA.
YA DAWO INDA YA SABA ZAMA,YANA ZAUNE CIKIN BAKIN CIKI SAI WANI ATTAJIRI YAZO YA,YI FAKIN DIN MOTAR SA KU SA DA INDA YAKE ZAUNE,YA FITO DAGA MOTA BAI KO CE WA KOWA KOMAI BA BALLANTANA SALLAMA,YA SHIGA BAYAN INDA SUKE A ZAUNE ,WATO WANI KANGO NE DAKE KUSA DASU,YAJE YA TSUGUNA YAYI FITSARI, YA TASHI YA DAWO YA DAUKI MOTAR SA YAJA YA TAFI,
TAFIYARSA KE DA WUYA SAI WANNA LABURA YA KEWAYA DOMIN YIN FITSARI,TSUGUNAWARSA KE DA WUYA SAI YAI IDO BIYU DA KUDI MASU YAWA,SAI YASA HANNU YA DAUKA.YA YI FITSARI YA TASHI YA KOMA INDA YAKE YA ZAUNA,YANA CIKIN TUNANIN KO NAWA NE KUDIN NAN KUMA ME YAKAMATA YAYI DASU,SAI GA ATTAJIRIN NAN YA DAWO FIRGICE YAI FAKIN KO KULLE KOFAR MOTA BAIYI BA YA SHIGA KANGON NAN A GUJE,SHI GARSA KE DA WUYA SAI YAJI MUTUMIN YANA CEWA DALA DUBU ASHIRIN DA BIYAR ACE TA BATA,ANYA KUWA KO ANAN NA ZUBAR ? SAI LABURAN NAN YA KA DA BAKI YACE WANI ABU KA YAR NE,SAI YA AMSA DA CEWA DALA DUBU ASHIRIN DA BIYAR NAZO NAYI FITSARI INA TAFIYA AMOTA NA MATSU NA RASAN INDA ZANYI SAI NA DAN RATSE NA ANAN,
SAI LEBURANAN YACE KO SUNE WADANNAN MUTUMIN YAYI AJIYAR ZUCIYA YA KAIWA KUDIN CHAFKA,LABURA YACE YI A HANKALI ABI TSARI DA DOKA.ATTAJIRI DAI KUDI SUKA TABBATA NASA NE ,YA MIKA MASA KUDIN SA SHI KUMA YA CE DA LABURA KA KYAUTA YA RATAYE RIGARSA YA JE ZAI SHIGA MOTA SAI GA WANI AL,MAJIRI YA ZO WUCEWA SAI DAUKO NAIRA DUBU YA IKAWA AL,MAJIRIN,LABURAN NAN YANA KALLO SHI KUMA KO KWABO BAI SAMU BA,HAKA DAI ALHAJI YAJA MOTARSA YA TAFI. WANNAN YIN DAI LABURA BAI SAMU KOMAI BA HAKA YA KOMA GIDA CIKIN YUNWA DA BACIN RAI GA LARUWA NA YA.YA DA KUMA MATARSA.

SHIN IN KAI NE YA,YA ZAKA BAIWA WANNAN ATTAJIRI KUDINSA ,KO KUWA YA ZAKA YI?

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on October 29, 2013 at 11:01am

MUTANE NE GUDA UKU KOWA YA NUNA BAJINTAR SA DA TSORON ALLAH DA KUMA NUNA KISHIN KASAR SA DA AL,UMMARSA.

NA DAYA-----SHI NE WANDA MAHAIFIYAR SA TAKE CIKIN MUMMUNAR RASHIN LAFIYA GASHI SHI MA,AIKACI NE NA GWAMNATI ,KUMA SHI KE KULA DA SHIGE DA FICE NA KUDIN MA,AIKATAR DA YAKE,KUMA WATA YA YI NISA DUK ABIN HANNUN SA YA KARE,YA DUBA BABU WATA KADARA DA YAKE DA ITA WADDA ZAI SAKA AKASUWA YA SAYAR,KUMA YA NEMI BASHI WAJEN ABOKAN ARZUKA DUK BA,A SAMU BA,MAHAIFIYARSA NA BUKATAR KARIN JINI A ASIBITI ROBA UKU,GA KUDIN GADO DA MAGUNGUNA DA AKA RUBUTA MASA.-----YA RASA YADDA ZAI YI ,ANA CIKIN WANNAN HALI NE SAI WANI MUTUM YAZO YACE MASA ZAI BASHI NAIRA DUBU DARI,AMMA YA SAKA MASA HANNU A BIYA SHI KUDIN SA DA YAYI WA MA,AIKATARSA AIKI,KUDIN SUN KAI MILIYAN BIYAR,AMMA FA MUTUMIN BAIYI AIKIN DA AKA BASHI YAYI BA.

IN KAI NE ZAKA SAKA MASA HANNU KO BAZA KA SAKA BA? ME NENE ABUN YI ANAN.?

Muna bukatar amsa sannan mukawo muku na biyu har zuwa na uku.
Mungode.

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 21, 2013 at 9:16pm

Kamar yadda muka yi bayani kwanakin baya a hasashen mu na cewa jam,iyyu da suka samu damar yin rijista da hukumar zabe ta kasa in sun cire son zuciya,tabbas zasu samu nasarori a zabeme zuwa wato 2015 in kuwa suka kuskura suka ki baiwa jama,a dama su zabi wanda ran su yake so to tabbas jam,iyya me ci ayanzu zata iya komawa kan karagar mulki.

To a yanzu dai an fara samun sabani tsakanin General Buhari da jam,iyyar APC kan nada wani daga cikin shugabannin jam,iyyar ta kasa,har ma Genaral ya yi furucin cewa zai bar jam,iyyar.
Hakan kuwa na iya kawo babbar matsala ga zaben 2015.
shin me ye ra,ayin ku a kan wannan yunkuri da General aka ce ya,yi.da kuma irin hasashen da wannan Dandali ya yi

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 20, 2013 at 3:49pm

Kowa yasan yadda siyasar kasan nan ke tafiyar wahainiya ta bangaren yadda ake tafiyar da ita cikin gaba da rashin lura da kuma rashin sassauci,yanzu ace baka da ra,ayin kanka sai na wani mutum guda sai abin da yace ayi za,ayi ko da dai- dai ne ko ba dai-dai bane? in kaki bin ra,ayin sa sai a neme ka da sharri, ko a cire ka daga gurbin aikin da kake yi,Wannan shi ne Gabar siyasa. me ye ra,ayinka a bisa irin wannan siyasa da aka zayyana, Tura ra,ayinka zuwa email a dandalintallafawamatasa@gmail.com

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 14, 2013 at 12:48pm

Hakika zaben 2015 zabe ne da manazarta na wannan dandali suka hango cewa za,ayi shi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa sakamakon makaoma dakowa yake ne mawa kansa a zaben shugaban kasa,kuma za,ayi mamaki,saboda sabbin jam,iyyu da suka fito mun yi nazarin cewa zasu sami kujeru da dama a wannan kasa idan har basu samu matsaloli a cikin su ba,kamar Tsayar da yan takara da kuma zaben shugabannin jam,iyyun .

Idan kuwa aka samu wadannan matasaloli to tabbas jamm,iyya me ci a yanzu zata iya komawa kan mulki ko da ba hakan ake so ba,Saboda haka ya zama wajibi Yan,siyasa masu san kawo sauyi a cikin kasa ta hanyar dimukuradiyya to su tabbata sun hada kansu waje daya kuma suyi kokari su baiwa masu san tsayawa takara dama ba tare da nuna iko ko isa ba,su bar jama,a su zabi wadanda suke zaton zasu kawo sauyi a kasa Najeriya don ci gaban mu baki daya.

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 11, 2013 at 5:35pm

Matasa sune ginshikin Rayuwa,dole su yi kuma subi a hankali wajen sanin mutuncin su da na iyayen su da kuma al,ummar su, Ana kiran matasa da manyan gobe saboda wataran sune manya sune masu fada aji kuma sune masu yin gargadi ga na baya su ne masu tsawatarwa matasan wannan lokacin da suka tsinci kansu a matsayin manyanta,sune masu bayar da Aure,sune masu san ganin kowa yayi mai kyau ya bar mara kyau,saboda haka ya kai matashi kabi a hankali wajen sani abubuwan da zaka din ga yi a ko wane lokaci kuma a ko wane irin yanayi. a guji yin aikin da zai janyo dana sani.Yi kokari ka shiga cikin kundin tarihi da za,a dinga tunawa da kai na Alheri.. Allah yasa mu dace

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 11, 2013 at 11:14am

Da yawan mutane musanman matasa suna da saurin jefa kansu cikin nadama sakamakon sauri-sauri ko kuma ince Gaggawa a duk abin da suka saka a zuciyarsu musanman ma idan aka zo maganar samun abin duniya,yana da kyau matasa su dinga hakuri, abi duniya sannu a hankali da kuma yin biyayya ga iyayen gidan su domin ta hakane zasu samu riba da kuma samun nasara a rayuwa.Gaggawa ta shaidan ce Jinkiri kuma na Allah ne Allah yasa mu dace da jinkiri Mai amfani, Ameen.

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 11, 2013 at 11:14am

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 11, 2013 at 11:14am

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 9, 2013 at 8:51pm

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 9, 2013 at 8:51pm
Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on September 9, 2013 at 8:41pm

YA ZAMA WAJIBI SHUGABANNI SU DINGA BAIWA YAN KASA HAKIIN DA YA RATAYA AKANSU TA KOWACCE SIGA,KO SABODA CEWA IN KAINE YAU GOBE BAKAI BANE,KUMA IN KA GAMA MULKIN CIKIN JAMA,A ZAKA DAWO KA ZAUNA TARE DASU.KAGA IN BAKAYI ABIN KIRKI BA BAZA KA IYA ZAMA CIKIN AL,UMMA BA.DAURE KA KAWO WA AL,UMMAR KA AIKIN CI GABA KO DAN SABODA KAIMA DA KAI ZA,A MORA. SAKO DAGA DANDALINTALLAFAWAMATASA.NING.COM

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on July 9, 2013 at 9:23pm

kamar yadda yan uwa suka sani cewa yau dinnan anga watan fara Azumin Ramadan,gobe kenan zamu tashi da Azumi na farko,Yakamata Muyi anfani da wannan damar wajen Rokon Allah ya yaye mana Musifun da suka addabi kasar nan,kuma mu tuba ga Allah, mu Roki Allah ya baiwa kasar nan Zaman lafiya ako ina,lungu da sako,Mu roki Rahamar sa, da Gafarar sa,Muyi wa yan uwa da suke cikin hali na kunci fatan Alheri mu kame bakin mu da munanan maganganu,mu yawaita aikin Alheri me kyau tare da sadaka,ziyarar juna,Mu yawaita istingifari,Hailala, da salatin Annabi( S.A.W) Mu daure mu yaki zuciyar mu muyi kyauta da abin da Allah ya bamu na dukiya.Mutaimaki duk me bukatar taimako ko da da kadan ne,Darajar dake cikin wannan wata Allah ya baiwa kowa ikon yin aikin Alheri,kuma Allah ya karbi Ibadun da zamuyi ,ya gafarta mana duk wani kuskure da zamu aikata bisa rashin sani ko kuma cikin dimuwa.

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on June 20, 2013 at 10:13pm

Matasa ku Daure ku dinga tunanin makaomar kasar ku da al,ummar ku da kuma kanku ,kar ku yarda ku bari ayi amfani daku wajen rusa alumma.sannan kuma kuyi kokarin jan,hankulan yan,uwan ku wajen tabbabatar da samar da zaman lfy ako ina kuka sami kanku,,.

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on June 20, 2013 at 10:12pm

Matasa ku Daure ku dinga tunanin makaomar kasar ku da al,ummar ku da kuma kanku ,kar ku yarda ku bari ayi amfani daku wajen rusa alumma.

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on June 19, 2013 at 9:23pm

Haka yake amfanin ilmi aiki da shi,,.

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on June 1, 2013 at 8:23pm

Hakika addu,a na da tasari ga masu imani da wadanda suka yadda da cewa Allah na karbar addu,a,mu ci gaba da yin addu,a a ko da yaushe domin samun saukin matsalar da muke ciki na rashin kwanciyar hankali komai ya fawa komawa dai-dai Saboda haka Mun gode Allah.

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on June 1, 2013 at 8:22pm

Videos

  • Add Videos
  • View All

Music

Loading…

Events

© 2017   Created by Dandalin Tallafawa Matasa.   Powered by

Badges  |  Report an Issue  |  Terms of Service

Live Support