MANUFOFI

 

DANDALIN TALLAFAWA MATASA DA WANZAR DA ZAMAN LAFIYA DON CI GABAN KASAR MU NIGERIA

 

 MANUFOFIN MU

An kafa wannan dandali domin tallafawa matasa da shawarwari na yadda zasu dogara da kansu,sannan  su taimaki al'ummarsu da kasar su, haka kuma da tattaunawa tare da yan majalisar wannan dandali masu kwazo da basira don wanzar da zaman lafiya don ci gaban  kasar mu  Nigeria.

Wannan dandali ba'a kafa shi da wata manufa don cin zarafin wani ko wata ba, zagi ko shagube na wani ko wata ba, habaici ko bakar magana ga wani ko wata ba, haka kuma duk dan wannnan dandali ya sani cewar wannan dandali nashi ne, saboda haka za'a tattauna abubuwa akan abin da suka  shafi matasa maza da mata, inganta rayuwarsu da tunano yadda zasu zama mutane na kwarai a kasa Nigeria.

 Bugu da kari wannan dandali zai tattauna yadda zamu samar da zaman lafiya a Nigeria lungu da sako na kasa baki daya musanman anan arewacin Nigeria inda aka fi magana da yaren Hausa,Fulani,Kanuri a garuruwa kamar: Kano, Kaduna, Zamfara, ,Bauchi, Gombe, Maiduguri, Yobe, Zaria, Jos, Adamawa, Sokoto, Kebbi,Taraba, Katsina, Jigawa, Minna, Abuja, Kogi,Benue, da  Nassarawa.

Al'umma da kasa basa samun cigaba sai da zaman lafiya da kwanciyar hankali,saboda haka ya zama wajibi mu yan Nigeria matasa maza da mata mu tashi tsaye domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a wannan kasa mai albarka da daraja a idon duniya wato Nigeria.

Taimaka da shawarwarin ka, sannan ka kasance kullum kana ziyartar wannan dandali domin bada taka gudunmawar na tabbatar da abubuwan da aka zayyana a sama.

 Tabbatar kayi rijista da wannan dandali kuma ka tabbatar ka janyo hankalin matasa masu kishin kasa cikin wannan dandali don bada tasu gudun mawar.

DOKOKIN MU SUNE :

 Babu maganar kwallon kafa ko fim ko siyasa ko hirar soyyayya da yan mata ko zagin shugabanni ko wata jinsin al'umma.

 TUNTUBE MU KAI TSAYE 

 dandalintallafawamatasa@gmail.com

 07037733303

IYAN-TAMA MULTIMEDIA LIMITED 

addreshinmu:  Shop No 17/18  rinji shopping complex sharada phase II Kano State Nigeria,

 

 

 

Bugu da kari wannan dandali ya kara fadada wannan shafi ta inda za,a iya magana akan shugabaci da shugabanni ta yadda za,a iya zuwa mana da batu me ma,ana wanda zai iya sa shugabannin mu su karu.Babu cin Fuska ko zagin wani Shugaba sannan babu habaici ko shagube.duk wanda ya karya dokar mu zamu cire rubutun da yayi. Mungode

Comment

You need to be a member of Dandalin Tallafawa Matasa to add comments!

Join Dandalin Tallafawa Matasa

Comment by MD usman Dawaki on April 28, 2013 at 5:08pm

,ina me farin cikin kasancewa ta a wannan shafi kuma zan bayar da gudun mawata kamar yadda aka tsara

Comment by Muhammad Dan-hajiya on March 20, 2012 at 4:48pm

Munji kuma munyarda da wadannan ka'idojin, to amma dai muna fatan hakan bazai hanamu damar bayyana gaskiyar abunda yake damun mu matasaba da irin hanyoyin dasuka dace domin tallafawa rayuwar matasa.

Comment by Muhammad Dan-hajiya on March 18, 2012 at 10:15am

Shin wadanne irin hanyoyi wannan dandali yakebi domin ganin cewa matasa sunsami cin moriyar irin tallafawar da akeson yimana? kuma yazuwa yanzu ko anfara tallafawa wasu matasan daga cikinmu? 

Comment by Umar Hussaini Kankarofi on March 13, 2012 at 2:36pm
Madalla da wannan dandali hakika wannan wata alama ce dake nuna samun cigaba ta fannin harkokin computer da communication, kuma hakika wannan dandali zai sake bunkasa harshen hausa da kuma kara masa kwarjini a idon duniya. Allah ya taimaki wadanda suka kirkiro wannan dandali, Allah ya kara basira
Comment by Muhammad Dan-hajiya on March 9, 2012 at 10:50am

 Menene hunkuncin duk wanda akasameshi da laifin  karya daya daga cikin dokokin wannan dandali?

Comment by Muhammad Dan-hajiya on March 9, 2012 at 10:48am

 Zaman lafiya shine babban tushen cigaban kowacce  al'umma, donhaka muna marhabun da wannan dandali domin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Comment by Sade Sa'idu Daura on February 9, 2012 at 10:41pm
Hakika mun gamsu da duk wannan dokokin, kuma da izinin Allah zamu zan masu biyayya ga wannan dokoki, mu dai fatan mu Allah yasa ya amfani al,ummar da akayi dansu, kai kuma jagoran A. Hamisu sai dai mu kara tayaka da addu,a ya Allah ya kara kaifin basira da hazaka fiye da wanda yake da kanfanin Apple na wayar salula. Mun gode.
Comment by Nura Kobi on January 28, 2012 at 2:20pm

Madalla ga wanna dandali mai albarka don wanzar da zaman lafiya da taimaka wa matasa, da fatan matasa zasu fa'idantu wajen ziyartan wannan dandali don tafka mahawara kan matsalolin da suka shige musu duhu.

Comment by Dandalin Tallafawa Matasa on January 5, 2012 at 2:14pm

Madalla da Muazu kuma munji dadin yadda ka amince da dokokinmu Allah ya bamu sa'a ameen

Comment by Mu'azu Hussaini Galadima on January 4, 2012 at 9:47pm

Insha Allahu za mu zama masu kiyaye dukkanin dokokin da aka tsara a wannan kungiya

Videos

  • Add Videos
  • View All

Music

Loading…

Events

© 2017   Created by Dandalin Tallafawa Matasa.   Powered by

Badges  |  Report an Issue  |  Terms of Service

Live Support