Al,ajabi--------Al,ajabi-----Al,ajabi
Yau ne da safe ina cikin mota na dawo daga daurin aure sai naga wani abin mamaki ,nazo zan gifta wani mai mota kirar Honda Accord ta zamani sai naga wani mai keken napep yana zagin wannan mai mota har takai sun yi fakin din Motar da kuma Babur din,mai keken napep ya ya fito ya tin kari mai mota yana tsaye har ya kama kwalar rigarsa ta wajen taga sai yaji an kirawo sunan sa ashe wanda ke gaban motar nan kanen baban sa ne,kuma a bayan motar Mahaifiyar sa ce akwance tana ta nishi hannuwan ta a daure da bandaji da kafafuwanta wani na rike da ita,sai yayi shiru ya rasa mai zaice,daga karshe dai ya yi ta maza ya ce mai ya faru mahaifiyar sa ta shi ga wannan hali,sai ta ka da baki tace da shi kai mukayi da kai zaka zo ka kaini gidan kanwar ka, sabo yau ne ake sunan dan ta na fari,kuma kasan nike zuwa na dora mata ruwa, nayi jira baka zoba sai na fito zan tare mai babur irin naka,wajan tsallaka titi sai wani mai babur din irin naka ya buge ni har na fadi,kuma ya bi ni ya rufe ni da duka,sai da mutane suka yi tara--tara a ka kamashi an kai shi wajen Hukuma yana can tsare,shi kuma wannan mai motar ban sanshi ba ya zo shi gewa ne yaga abin da ya faru shi ne ya dauke ni ya kaini asibiti aka dora ni kuma ya biya mun magani yanzu muna hanyar mu ta komawa gida ne kai kuma kazo ka goge masa mota ya yi magana kuma kake ta zagin sa har kazo kaci kwalar rigarsa sai uwarnan ta fasheda kuka ta kara fashewa da kuka.........

In kai ne ya ya zakayi,kuma me zaka ce da mutumin nan? Sannan kuma in kai ne Mai motar wane mataki zaka dauka. Sannan wane darasi mai wannan Babur ya gani da idon sa.?

Views: 57

Comment

You need to be a member of Dandalin Tallafawa Matasa to add comments!

Join Dandalin Tallafawa Matasa

Videos

  • Add Videos
  • View All

Music

Loading…

Events

© 2017   Created by Dandalin Tallafawa Matasa.   Powered by

Badges  |  Report an Issue  |  Terms of Service

Live Support